1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekara guda da juyin mulki a Guinea

September 6, 2022

Majalisar sojojin Guinea ta cika shekara guda a kan madafun ikon kasar, bayan juyin mulkin da suka yi wa tsohon shugaban kasar Alpha Conde.

https://p.dw.com/p/4GUSq
Guinea | Kanal Mamady Doumbouya
Shugaban gwamnatin mulkin soja ta Guinea Conakry Kanal Mamady DoumbouyaHoto: Xinhua/imago images

A yayin da suka karbe mulkin dai, sojojin karkashin jagorancin Kanal Mamady Doumbouya sun shimfida tsare-tsare da dama da suka hadar da karbe dukiyar kasa daga hannun 'yan siyasa da hana 'yan farar hular kasar yin jerin gwono tare rushe kawancan 'yan faftuka na FNDC. Bayan juyin mulkin da sojojin suka yi wa gwamnatin mutu ka raba ta tsohon shugaban kasar Alpha Conde majalisar gwamanatin rikon kwarya ta sojojin ta gana da 'yan kasar daga sassa dabam-dabam, saidai wannan ganawa tsakanin wani bangaran 'yan siyasa da sojojin a yanzu ba za a ce ta haifara wani abin azo a gani ba. Hakan ta sanya bangarorin biyun, gaza jituwa a tsakaninsu. Jam'iyar madugun 'yan Adawa Cellou Dalien Diallo ta CNRD, na yi wa sojojin kallon masu yin mulkin kama karya.

Guinea | Alpha Condé
Alpha Conde dai ya kwashe tsahon shekaru yana mulki a Guinea ConakryHoto: John Wessels/AFP

A sanarwarsa ta farko a yayin fara mulki bayan tumbuke gwamnatin ta Conde dai, Kanal Mamady Doumbouya  ya sha alwashin cewa babu wani  dan kasa da zai mutu sanadiyyar fadar albarkacin bakinsa. Sai dai a yanzu mutane da dama na tsare a gidan kaso, sakamakon fadar albarkacin bakinsu. A farkon watan mayu da ya gabata shugaban majalisar rikon kwaryar kasar ta Guinea ya kayyade wa'adin mulkinsu na watanni 39 zuwa 36. 'Yan siyasar kasar da kungiyar Habaka Tattalin Arzikin Yankin Afirka ta Yamma wato ECOWAS ko CEDEAO sun yi watsi da wannan bukatar, nan take kuma kungiyar ta tura tsohon shugaban kasar Benin Thomas Boni Yayi a matsayin mai shiga tsakani a Guinea. Thomas Boni Yayi ya kammala aikin shiga tsakani, inda ya yi yunkurin haduwa da bangarorin baki daya na faran hulla da 'yan siyasa da ma masu rikon kwaryar. Abin jira a gani dai, shi ne rahoton da zai mika wa kungiyar ta ECOWAS ko CEDEAO.