1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rushe kungiyar kwancen adawa a Guinea

August 10, 2022

Gwanmnatin mulkin soji ta Guinea Conakry ta rusa kungiyar kawancen da ta hadar da 'yan siyasa da kungiyoyin farar hula da kuma kwadogo da ke adawa da gwamnatin wato FNDC.

https://p.dw.com/p/4FNvp
Guinea | Mamady Doumbouya
Shugaban gwamnatin mulkin soja ta Guinea Conakry Mamady Doumbouya Hoto: Kommunikationsdienst der Präsidentschaft von Guinea

Kungiyar kawancen da ta jagoranci zanga-zangar adawa da tsohon shugaban kasar Alpha Condé bayan da ya yi tazarce ta bujirewa sojojin, watannin kadan bayan juyin mulkin da suka yi da kuma ke nuni da cewar ba su da niyyar mika mulki ga farar hula. A cikin wata sanarwa da ministan cikin gida na kasar ta Guinea ya fitar, ya ce kungiyar na yin barazana ga zaman lafiya da hadin kan kasa tun lokacin da aka kafata a shekara ta 2019. Sai dai wani dan siyasa Bah Oury ya ce rusa kungiyar take hakkin dimukuradiyya ne. A cikin watan Yulin da ya gabata, kamewa tare da tsare wasu shugabannin kungiyar guda uku da hukumomi suka yi, ya haifar da kazamin fada tsakanin kungiyoyin matasa da 'yan sanda.

Guinea | FNDC | Zanga-Zanga
Kungiyar FNDC ta ce ba za ta daina zanga-zanga ba har sai sojoji sun mika mulkiHoto: CELLOU BINANI/AFP/Getty Images

Tun da fari kungiyar Habaka Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma wato ECOWAS ko CEDEAO ta yi kira ga hukumomin Guinea da kungiyoyin siyasa da farar hula da su shiga tattaunawa, domin kwantar da tarzoma tare da cimma matsaya kan jadawalin zabe da kuma hanyoyin da suka dace a kokarin maido da tsarin mulkin dimukuradiyyar cikin lumana. Farfeser Mory Condé wani masanin harkokin sharia da kundin tsarin mulki, ya ce gwamnatin ta yi babban kuskure. Sojojin da ke rike da madafun ikon Guinea sun yi alkawarin mika mulki ga farar hula a cikin shekaru uku, sai dai kungiyar ta ki amincewa. Duk da cewar gwamnati ta haramta kungiyar, amma kawancen na FNDC ya sha alwashin gudanar da babban gangami a makon gobe domin tilastawa shugabannin mulkin sojan mika mulki ga farar hula cikin gaggawa.