1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Guinea za ta mika ragama ga farar hula

July 21, 2022

Sabon shugaban karba-karba na kungiyar ECOWAS ko CCEDEAO Umaro Sissoco Embaló na Guinea- Bissau, na lalubo hanyar mayar da kasar Guinea Conakry mulkin dimukaradiyya.

https://p.dw.com/p/4EUCk
Guinea-Bissau | Umaro Sissoco Embaló | Ruwanda
Sabon shugaban karba-karba na ECOWAS Umaro Sissoco Embaló na Guinea- BissauHoto: Pressebüro der Präsidentschaft der Republik Guinea-Bissau/Jakadi

Yayin ziyarar kwanaki biyu da ya kai birnin Conakry, Shugaba Umaro Sissoco Embaló na Guinea- Bissau kana shugaban karba-karba na kungiyar ta ECOWAS ko CCEDEAO ya tattauna da gwamnatin mulkin sojan Guinea tare da mai shiga tsakani kana tsohon shugaban kasar Benin. Amma 'yan siyasa sun dage cewa a gudanar da tattaunawar kasa, domin warware rikicin. Mai shiga tsakani na kungiyar ECOWAS ko CEDEAO kan shirin mika mulki ga farar hula a kasar Guinea Conakry, wanda ya kasance tsohon shugaban kasar Jamhuriyar Benin Thomas Boni Yayi ne ya fara isa birnin na Conakry kafin shugaban kasar Guinea-Bissau Umaro Sissoco Embaló.

Karin Bayani: Matakan ECOWAS kan Burkina Faso da Mali

Shi ma sabon shugaban hukumar zartaswa na ECOWAS, Omar Alieu Touray dan asalin kasar Gambiya ba a bar shi a a baya ba. Dukkanin manyan jami'an sun samu tarba ta arziki, daga Kanal Mamady Doumbouya shugaban gwamnatn mulkin soja wanda ya gana da su. Daga bisani kuma sun tattauna da Bernard Gomou wanda ya wakilci firaminista Mohamed Béavogui sakamakon wata ziyarar aiki da yake yi a kasar waje da kuma sauran mambobin gwamnatinsa.

Guinea | Mamady Doumbouya
Shugaban gwamnatin mulkin soja ta Guine Conakry, Kanal Mamady DoumbouyaHoto: Kommunikationsdienst der Präsidentschaft von Guinea

A daya hannun kuma, tawagar ta ECOWAS ko CEDEAO ta gana da shugaban kasa da 'yan majalisar dokoki na rikon kwarya a Guinea da kuma jami'an diflomasiyya na kasashen Faransa da Amirka da Jamus da Japan da kuma Italiya. Diao Baldé shugaban jam'iyyar Union Pour la Guinée Nouvelle (UGN) da ke cikin kawancen jam'iyun adawa na  (Anad), ya ce ba a nan gizo ke saka ba. Dan siyasar ya ce akwai bukatar gudanar da tattaunawa ta kasa, domin samun mafita ga rikicin da ake fama da shi tare da mayar da mulki a hannun farar hula.

Karin Bayani:Sojojin Mali sun sake wa'adin mika mulki ga farar hula

Sai dai Aboubacar Demba Diabi masanin kimiyyar siyasa kuma  malami a jami'ar Gamal Abdel Nasser ta Conakry ya ce kusantar juna tsakanin gwamnatin mulkin soja da 'yan siyasa zai yi wuya, saboda gurfanar da wasu manyan masu fada a ji a siyasar kasar da aka yi a gaban kuliya. A cewar masanin dai, gibin da ke tsakanin bangarorin masu rikici da juna na da fadi sosai. Kanal Mamady Doumbouya wanda ya hambarar da shugaba Alpha Condé na Guinea Conakry bayan shafe sama da shekaru 10 a kan kujerar mulki, ya yi alkawarin mika mulki ga zababbiyar gwamnatin dimukuradiya cikin shekaru uku. Sai dai kungiyar ECOWAS ko CEDEAO ta yi watsi da wannan jadawali, tana mai neman a takaita lokacin gudanar da zaben.