1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojojin Mali sun sake wa'adin mika mulki ga farar hula

Mouhamadou Awal Balarabe M.Ahiwa
June 7, 2022

Gwamnatin soji a Mali, ta kayyade wa kanta wa'adin watan Maris na shekarar 2024 domin mika mulki ga hannun farar hula, bayan dokar da ta shata shekaru biyu na wa'adin mika mulkin. Sai dai hakan ya janyo rarrabuwar kanu.

https://p.dw.com/p/4CNa5
Mali | Colonel Assimi Goita
Hoto: Malik Konate/AFP

Sanarwar ta gwamnatin Mali ta zo ne kwanaki biyu bayan wani taron koli da ECOWAS ko CEDEAO ta kammala, ba tare da dage takunkumi mai tsanani kan harkokin kasuwanci da na kudi da ta kakaba wa kasar ba. Ita dai kungiyar ta yammavin Afirka tana matsa wa Assmi Goita da mukarrabansa ne lamba domin su gabatar da jadawalin shirya zabe tare da mayar da mulki hannun farar hula.

Kanar-kanar na Mali da suka karbi ragamar mulkin kasar da karfi a watan Agustan 2020 cikin mummunan yanayin tsaro da siyasa, sun fara janyewa daga alkawarin da suka yi na mayar da kasar kan turbar dimokuradiyya a watan Fabrairun da ya gabata. A maimakon haka suka shirya gudanar da mulki na tsawon shekaru biyar. Sai dai halin tsaka mai wuya da takunkumi ya jefa Malin, ya sa gwamnatin mulkin soji rage wa'adin mulkinta zuwa watanni 24, farawa daga 26 ga watan Maris na 2022. Ministan harkokin wajen Mali Abdoulaye Diop ya tabbatar da wannan mataki a tashar talabijin din kasar.

"Muna maraba da rahoton da mai shiga tsakani Goodluck Jonathan ya gabatar, wanda ya dogara kan shawarwarin da gwamnatin Mali ta bayar, wadanda suka shafi wa'adin mulkin rikon kwarya. Gwamnati ta bada shawarar wa'adi watanni 24 farawa da Maris din 2022 zuwa Maris din 2024. Mun fahimce cewar an mika wannan rahoto, kuma taron kolin ya tare shi hannu bi-biyu."

Nigeria | ECOWAS Gipfel
Hoto: Präsidentschaft von Niger

Sai jadawalin zabe na gwamnatin Mali ya sha banban da wanda ECOWAS ta amince da shi na watanni 16. Hasali ma shugabannin na yammacin Afirka sun yanke shawarar ci gaba da tattaunawa da Mali don cimma matsaya kan zabe kafin su soke takunkumin da suka aza mata. Saboda haka ne manyan jami'an kungiyar suka yi mamakin matakin na gwamnatin Bamako domin sun tura mai shiga tsakani tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya gana da bangarori daban-daban domin a fuskanci alkibla daya.

Wasu masharhanta na cewa sojojin na Mali sun yi riga Malam masallaci, amma 'yan adawa da 'yan farar hula na Mali na san barka saboda sabon jadawalin zai sa a kawar da takunkumin da aka kakaba mata, a cewar Chaibou Oumarou, wani dan Nijar mazaunin Bamako na Mali.

Gwamnatin mulkin sojin Mali na fatan ECOWAS ta dage takunkumin da ta aza mata a taron da za ta gudanar a watan Yuli domin ta samu sa'ida. Amma rabuwar kawuna ya sa shugabannin sun jinkirta yanke shawara zuwa wani sabon taron koli da zai gudana a ranar 3 ga Yuli. Amma ana jira a ga tasirin dokar ta Mali a kan shawarar kungiyar ECOWAS, kasancewa a lokacin da za su gudanar da taron kolinsu a watan Yuli, watanni 20 da rabi za su rage kafin lokacin da aka kayyade na mika mulki ga farar hula a Mali a watan Maris na 2024.