1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasar Guinea bayan juyin mulkin soja

Suleiman Babayo LMJ
September 7, 2021

Sojojin da suka kwace madafun iko a kasar Guinea Conakry suna kara karfafa matsayinsu, ta hanyar nada sojoji jagorancin yankunan kasar da kuma kakkabe hannun manyan jami'an tsohuwar gwamnati daga tafiyar da ita.

https://p.dw.com/p/402rl
Videostill | Guinea Conakry - Militärputsch: Doumbouya hält Ansprache
Jagoran juyin mulkin kasar Guinea Conakry, Mamady DoumbouyaHoto: AFP

Barazanar takunkumi daga kungiyar Habaka Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma ECOWAS da shugabannin kasashenta ke shirin taron gaggawa, kan halin da ake ciki a kasar ta Guinea bayan sojojin sun kifar da gwamnatin Shugaba Alpha Conde bai hana masu juyin mulkin nada mukaman ba. Tuni Kanar Mamady Doumbouya wanda ya jagoranci juyin mulkin ya fara daukar matakai, bayan alkawarin hada kan 'yan kasa da samar da ci-gaba gami da tsari mai karbuwa ga daukacin al'ummar kasar.

Karin Bayani: Sojoji sun yi juyin mulki a Guinea Conakry

Sabuwar gwamnatin mulkin sojan ta Guinea ta bayar da umurni ga mai-gabatar da kara na gwamnati, ya tattara bayanai kan duk wadanda aka kama kan dalilai na siyasa domin a sake su cikin gaggawa. Wannan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da Kanal Amara Camara mamba a sabuwar gwamnati ya karanta, a tashar talabijin din kasa. "Shugaban majalisar dawo da ci-gaba a Guinea, ya umurci sakataren ma'aikatar shari'a da babban mai gabatar da kara su tattara takardun wadanda aka kama saboda dalilai na siyasa, domin sakin su cikin kankanin lokaci."

Guinea Conakry | Videostill von mutmaßlicher Festnahme von Guineas Präsident Alpha Conde durch Militäreinheiten
Mai shekaru 83 a duniya, Alpha Conde ya rasa mulkin kasar Guiea bayan juyin mulkiHoto: AFP

A wata hira da ya yi da tashar DW, jagoran 'yan adawa na kasar Cellou Dalein Diallo wanda ya fuskanci musgunawa karkashin tsohuwar gwamnatin Alpha Conde da sojoji suka kifar, ya ce a shirye yake ya ba da taimakonsa kan tabbatar da dimukuradiyya da dawo da martabarta a kasar. A cewarsa duk da cewa ya jijjiga sakamakon juyin mulkin, amma tsohon shugaban shi ne ya gaza bin dokokin kasa da janyo wannan yanayin da Guinea ta samu kanta a ciki, yana mai cewa gwamnatin ta kasance wadda ta kashe 'yan Guinea da ke zanga-zanga a kan ka'ida, kuma tsohon shugaban ya mayar da kansa komai ya yi shi ne daidai.

Karin Bayani: Sakamakon zaben Guinea ya bar baya da kura

Shi dai Alpha Conde mai shekaru 83 a duniya tsohon dan-adawa ya lashen zaben shugaban kasa na shekara ta 2010 kuma zaben dimukuradiyya na farko. Ya sake samun wa'adin shekaru biyar a shekara ta 2015, amma a shekarar da ta gabata ta 2020 bayan kammala wa'adi na biyu kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada tare da sallama da madafun iko, gabanin zaben kasar hambararren shugaban ya yi gyara ga kundin tsarin mulki domin samun tazarce, abin da ya saba da kundin tsarin mulkin da ya yi rantsuwa da shi tun da farko. Matakin nasa dai, ya jefa kasar ta Guinea Conakry da ke yankin yammacin Afirka cikin rudanin siyasa.