Goyon bayan Iran ga firmanistan Iraki | Labarai | DW | 06.07.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Goyon bayan Iran ga firmanistan Iraki

Iran ta jaddada goyon bayanta ga firaministan Iraki Nuri al-Maliki sai dai Iran din ta ce za ta iya sauya matsayi in majalisar dokokin Irakin ta zabi wani mutum na daban.

Gwamnatin Iran ta ce ta na goyon bayan cigaba da kasancewar Nuri al-Maliki a matsayin firaministan Iraki sai dai ta ce za ta iya sauya ra'ainta kan wannan batun in har majalisar dokokin kasar ta zabi wani mutum na daban don kasancewa firaminista.

Iran din ta ce ba za ta yadda da duk wani shiri na ganin a raba kasar ba don haka ko wanne mutum aka zaba a matsayin firaminita za ta yi aiki da shi domin tabbatar da dorewa kasar a matsyin tsintsiya madaurinki daya.

A ranar Talatar mai zuwa ce dai majalisar dokokin Irakin za ta yi wani zama inda ake sa ran za ta zabi kakakinta da ma dai sabon firaministan da zai jagoranci kasar wadda a halin yanzu ke fama da tada kayar baya ta 'yan kungiyar nan ta Sunni ta ISIS da ke son kifar da gwamnati da kuma 'yan Kurdawa da ke rajin ballewa daga kasar.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Ummaru Aliyu