1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Gowon ya bukaci dage takunkumin da ke kan Nijar

February 22, 2024

A yayin da ake ci gaba da fuskantar kalubale na wanzuwar ECOWAS a matsayin tsintsiya daya, tsohon shugaban Najeriya da ya taimaka wajen kafa kungiyar Yakubu Gowon ya bukaci janye takunkumai ga kasashen da suka fice.

https://p.dw.com/p/4ciyp
Tsohon shugaban mulkin sojan Najeriya Janar Yakubu Gowon
Tsohon shugaban mulkin sojan Najeriya Janar Yakubu GowonHoto: imago/ZUMA/Keystone

Tsohon shugaban na Najeriya Janar Yakubu Gowon ya jaddada matsayarsa kan bukatar janye wa kasashen Burkina Faso da Guinea da  Mali da kuma Jamhuriyar Nijar takunkumai, tare da neman kasashen da su sake yin nazari kan matakin da suka dauka na ficewa daga Ecowas, kasancewar dukkaninsu uku na da cikin mambobin da suka kafa kungiyar a 1975.

Karin bayani:Martanin kasashe kan ficewar wasu daga ECOWAS

Gowon ya furta hakan ne a wani taro da kungiyar ECOWAS ta jagoranta a Abuja babban birnin Najeriya gabanin taron shugabannin kungiyar da za a gudanar don tattauna rikicin siyasar yankin yammacin Afirka. Shi dai Janar Gowon da ya jagoranci yakin basasar Najeriya da 'yan awaren Biafra, ya gana da shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu kafin ya gabatar da jawabi a wajen taron.

Karin bayani:Nijar: ECOWAS za ta tattauna da sojoji

Shugaban hukumar ta ECOWAS Omar Alieu Touray ya ce Gowon ya aiki da sako mai muhimmanci kuma ya sha alwashin isar da sako a taron koli na shugabannin kasashen kungiyar Ecowas.