Yakubu Gowon tsohon Janar a rundunar sojojin Najeriya, kana tsohon shugaban kasa, wanda aka yi yakin basasa lokacin da yake rike da mulki.
Ya yi nasara lokacin yaki na hana Najeriya rabewa. Gowon ya zama mafi karancin shekaru da ya karbi madafun ikon Najeriya, lokacin yana mukamun Kanar na sojoji.