1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ko Jonathan zai yi takara a zaben Najeriya?

September 26, 2025

Tsohon shugaban Kasar Najeriya Goodluck Ebele Jonathan ya gana da shugaban jam'iyyar ADC. Wata alama da ake ganin ta sake dawowa cikin harkokin siyasa.

https://p.dw.com/p/518Oy
 Goodluck Jonathan
Goodluck Jonathan Hoto: AP

A shekara ta 2015 ne Jonathan ya zamo shugaban kasar na farkon fari da ya karbi kaddamar shan kaye cikin fage na siyasar  Najeriya, ya kuma mika mulki ga adawa. 

Duk da cewar dai an dade ana ta zawarci na tsoho na shugaban Najeriyar cikin gidan na adawa, wannan  ne karo na farkon fari da Goodluck Ebele Jonathan yake nuna alamu na sake komawa cikin fagen na siyasar  Najeriya a kai tsaye .

Tsohon hoto na ajiya na Goodluck Jonathan
Tsohon hoto na ajiya na Goodluck Jonathan Hoto: picture-alliance/dpa

Kuma wata ganawa a tsakaninsa da shugaban jam'iyyar ADC ta adawar David Mark dai yanzu haka na jawo ka ce na ce cikin fagen siyasa da ke dada nuna alamun zafi.

Ana dai kallon tsoho na shugaban da ke da dimbin mabiya a sashensa na kudu maso kudanci na kasar na cikin sahun gaba a masu siyasa ta kasar da ke iya karbar mulki a wurin jam'iyyar APC.

Hira da Aminu Waziri Tambuwal

Kokari na kare magana ko kuma bude sabon babi cikin fage na siyasar tarayyar Najeriyar, a  baya dai mai dakinsa   Patience Jonathan ta ce maigidan nata ya gama da siyasar  Najeriyar har abada. Kafin wata  nasara ta aboki a Kasar Ghana daga dukka na alamu ta nemi sauya tunani na tsoho na shugaban  Najeriyar.

Ndume: Wasu na gurbata siyasar Najeriya

Jonathan da Mahama dai sun sha kaye a a kujera ta shugaban kasar a kasashensu, to sai dai  kuma can a kasar Ghanan John Mahama yai nasarar sake karbar mulki – daga hannun jam'iyyar data kada shi ta karbe mulkin.

Goodluck Jonathan
Goodluck JonathanHoto: Getty Images/AFP/P. U. Ekpei

Ya zuwa yanzun dai tsoho na shugaban ya bi gari yana ta neman afuwar wadanda suke da tunanin ya  bata tare da aiyyana yafiya bisa laifin da aka yi masa, a wani abun da ke nuna alamun tunkarar fagen siyasa na kasar a kai tsaye.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani