1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gobara ta salwantar da rayuka a Aljeriya

August 18, 2022

Mutane da dama ne bayanai ke cewa sun salwanta a Aljeriya wasu masu yawa suka jikkata sakamakon wutar daji da ke ci a larduna 14 na kasar iyaka da Tunisiya.

https://p.dw.com/p/4Fgjh
Algerien Waldbrände
Hoto: Algerian Civil Defense/AA/picture alliance

Akalla mutane 26 ne rahotanni ke tabbatar da salwantar su sakamakon wutar daji da ta tashi a yankin arewa maso gabashin kasar Aljeriya.

Ministan harkokin cikin gida a Aljeriya, Kamel Beldjoud ya ce a lardin Al Tarf kadai, mutane 24 wutar ta kashe, yayin da a lardin Setif aka rasa mutum biyu.

Akwai ma wasu gomman da suka jikkata sakamakon kuna da kuma shakar hayaki mai tsanani da suka yi.

Hukumomi a Aljeriyar sun ce yankuna 39 ne ke fama da gobarar ta daji a cikin larduna 14, kuma 16 na a lardin Al Tarf ne.

Garin Sou Ahras, wanda ke iyaka da kasar Tunisiya ma na fama da gobarar da kawo yanzu jami'an kwana-kwana ta sauran jirage masu saukar angulu ke kokarin kawo karshenta.