Gobara a China ta hallaka mutane da dama | Labarai | DW | 13.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gobara a China ta hallaka mutane da dama

Tashin wata gobara a wani rukunin masana'antu a kasar China ya yi sandin asarar rayuka da ta dukiya mai dimbin yawa.

Jami'an tsaro a kasar sun killace inda wannan lamari ya wakana a Tianjin da ke arewacin kasar kuma sun mutanen da suka jikkata sun dari hudu.

'Yan sanda sun hana jama'a musamman ma manema labarai kaiwa ga inda abun ya wakana, yayin da wasu al'ummar kasar ke zargin ana share sakonnin da suka sanya kan wannan batu a kafofin sada zumunta irinsu Twitter da Facebook.

Hotuna a shafukan intanet sun nuna yadda gobara ta yi ta'adin gaske a yankin sandiyyar fashewar wasu abubuwa da ake zaton sinadarai ne masu hadari.