Girka zata samu rancen kuɗi Euro miliyan dubu 110. | Labarai | DW | 03.05.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Girka zata samu rancen kuɗi Euro miliyan dubu 110.

Ƙungiyar ƙasashen dake amfani da Euro sun ɗauki matakin farfaɗo da tattalin arziƙin Girka.

default

Ministocin kuɗi na ƙasashen dake yin amfani da takardar kuɗi ta Euro, sun cimma daidaito akan yawan kuɗin tallafin da zasu baiwa ƙasar Girka a matsayin rance. A lokacin daya ke magana ga wani taron manema labaran daya kira a birnin Brussels, hedikwatar tarayyar Turai, shugaban gungun ƙasashen dake yin amfani da takardar Euron, wanda kuma shi ne Frime ministan ƙasar Luxembourg Jean - Claude Juncker, ya bayyana cewar jimillar kuɗin zai kai Euro miliyan dubu 110 ne cikin shekaru ukku masu zuwa. Gungun ƙasashen dake yin amfani da Euro ne zasu samar da miliyan dubu 80 daga cikin adadin, a yayin da asusun bayar da lamuni a Duniya na IMF kuma zai samar da sauran kuɗin.

Juncker ya jaddada cewar, rancen na tattare da tsauraran ƙa'idoji, waɗanda kuma shugaban hukumar tarayyar Turai Hose Manuel Barroso ya ce, sun gamsu dasu:

" Hukumar tarayyar Turai na ganin cewar, a yanzu an cimma sharuɗɗan da Turai ta gindaya domin baiwa Girka rance. Muna so kuma mu bayyana a fili cewar, za'a biya dukkan buƙatun ƙasar Girka."

Sai dai duk da wannan matakin da ministocin kuzɗin suka ɗauka, kuɗin Euro na ci gaba da faɗuwa a kasuwannin musaya na Duniya, kamar yadda aka gani a hada hadar data gudana da safiyar wannan Litinin.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Zainab Muhammad Abubakar