Girka ta soma sauke bashin da ke kanta | Labarai | DW | 20.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Girka ta soma sauke bashin da ke kanta

Girka ta samu sukunin biyan bashi sakamakon wani sabon bashin na sama da biliyan bakwai na Euro da ta samu daga kungiyar EU a karshen makon da ya gabata

Kasar Girka ta kama hanyar soma biyan kudaden bashin da ke a wuyanta inda tun a yau litanin za ta sauke bashin kudi kimanin biliyan biyu na Euro ga Asusun bada Lamani na Duniya na IMF da kuma wasu kudi sama da biliyan hudu ga bankin raya kasashen Turai. Kasar ta samu sukunin biyan wadannan kudaden bashi ne a sakamakon wani sabon bashin na kudi sama da biliyon 7 na Euro da ta samu a karshen makon da ya gabata daga Kungiyar Tarayyar Turai.

Hakazalika kasar za ta biya wasu kudaden bashin na miliyon 500 na Euro da ta karba daga hannun babban bankin kasar wanda wa'adin biyan ya kawo karshe tun a karshen watan Yunin da ya gabata. Bashin da zai saura ga kasar ta Girka bai taka kara ya karya ba kuma nan zuwa karshen wata lamurra za su koma daidai a kasar.