Gina majalisa zai lashe dala miliyan 200 a Ghana | Labarai | DW | 04.07.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gina majalisa zai lashe dala miliyan 200 a Ghana

Gwamnatin kasar Ghana ta kare shirinta na kashe dala miliyan 200 kan aikin gina sabuwar majalisar dokokin kasar, duk da adawa da kudirin ke fuskanta daga al'umma.

Kungiyoyin fararen hula sun kaddamar da kamfe a yanar gizo mai taken #Dropthatchanber wato a jingine batun gina sabuwar majalisa. A cewar kungiyoyin akwai muhimman bukatu da suka sha gaban ginda sabuwar majalisa.

Hukumomi a kasar Ghana na da muhimmanci domin fadada kujerun majalisar daga 275 zuwa kujeru sama da 400. Kasar ta Ghana za ta ranto kudaden aiwatar da aikin ne daga kasar Indiya. Sai dai batun na cigaba da haifar da muhawara tsakanin 'yan kasar da wajen kasar.