1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Labarin Wasanni 23.01.2023

Lateefa Mustapha Ja'afar RGB
January 23, 2023

A kokarinta na ci gaba da zama daram bisa teburin gasar Premier League ta Ingila, Arsenal ta lallasa Manchester United a yayin da Iraki ta yi nasara a gasar kwallon kafa ta kasashen yankin Gulf.

https://p.dw.com/p/4Mag1
Wolfsburg ta lallasa Freiburg da 6-1
Wolfsburg ta lallasa Freiburg da 6-1Hoto: Gerd Gruendl/Beautiful Sports/imago images

A kokarinta na ci gaba da zama daram bisa teburin gasar Premier League ta Ingila, Arsenal ta lallasa Manchester United da ci uku da biyu. Shekaru 35 ke nan rabon da Iraki ta halarci gasar kwallon kafa na kasashen yankin Gulf, sai dai kuma ta bayar da mamaki ta hanyar lashe gasar bayan ta doke Oman a wasan karshe.

A karshen mako an yi ruwan kwallaye a gasar bundesligar kasar Jamus. A wasannin da aka fafata a mako na 16, Bayern da ke zaman ta daya a teburin bundesligar ta bana ta tashi kunnen doki daya da daya a wasan da suka fafata da Leipzig. A wasannin da aka kara a ranar Asabar kuwa, Eintracht Frankfurt ta caskara Schalke da ci uku da nema, kana Bochum da lallasa Hertha Berlin da ci uku da daya. A birnin Stuttgarta kuwa, an tashi wasa kunnen doki daya da daya ne tsakanin Stuttgart din da Mainz, kana Wolfsburg ta yi wa Freiburg dukan kawo wuka da ci shida da daya kamar yadda ta kaya a gidan FC cologne, inda ta yi wa Werde Bremen likis da ci bakwai da daya. Ita ma Union Berlin ta lallasa bakuwarta Hoffenheim da ci uku da daya.

Jude Bellingham na Borussia Dortmund
Jude Bellingham na Borussia DortmundHoto: Moritz Müller/imago images

 A wasannin da aka fafata a Lahadin karshen mako kuwa, Borussia Dortmund ta karbi bakuncin Augsburg tare da caskara ta da ci hudu da uku yayin da takwararta Borussia Mönchengladbach ta sha kashi a gida a hannun Bayern Leverkusen da ci uku da biyu. Har yanzu dai Bayern ce ke kan teburin na Bundesliga da maki 35, yayin da kungiyoyin Frankfurt da Union Berlin ke biye mata a matsayi na biyu da na uku da maki 30 kowaccensu.

A gasar Premier League ta Ingila kuwa, an tashi wasa canjaras babu ci tsakanin Liverpool da Chelsea yayin da Westham United ta karbi bakuncin Everton kuma ta caskara ta da ci biyu da nema. An tashi wasa babu ci tsakanin Leeds United da Brentford kana Manchenster City ta samu nasara da ci uku da nema a kan Wolverhampton da ta kai mata ziyara. Ita kuwa Arsenal ta samu nasara ne a kan abokiyar hamayyarta Manchenster United da ci uku da biyu, wanda hakan ya ba ta damar ci gaba da zama daram a saman tebur da maki 50 yayin da Manchenster City ke biye mata da maki 45. Newcastle United na matsayi na uku da maki 39 bayan da ta tashi wasa canjaras babu ci da kungiyar Crystal Palace. Yayin da Manchester United ke matsayi na hudu ita ma da maki 39.

A laligar kasar Spain kuwa, Bercelona ta samu nasarar doke abokiyar hamayyarta Real Madrid bayan ta samu nasara da ci daya mai ban haushi a kan kungiyar kwallon kafa ta Gatafe. Duk da cewa Real Madrid din ita ma ta samu nasarar a kan takwararta Athletic Bilbao da ci biyu da nema, hakan bai sa ta koma saman teburin na laliga ba. Ita ma Sevella ta samu nasara da ci daya da nema a kan Cadiz yayin da Atletico Madrid ta lallasa Real Valladolid da ci uku da nema. A yanzu haka dai Bercelona ke saman tebur da maki 44 yayin da Real Madrid ke biye mata a matsayi na biyu da maki 41 sai Real Sociedad a matsayi na uku da maki 38.

Irak | 25. Golfmeisterschaft in Basra | Irak - Oman
Irak ta doke Oman a gasar kwallon kafa ta yankin GulfHoto: Thaier Al-Sudani/REUTERS

Bayan shekaru 35 rabonta da shiga gasar kwallon kafa ta kasashen yankin Gulf, kasar Iraki da a karon farko ta karbi bakuncin gasar ta yi nasarar zama zakara bayan doke kasar Oman da ci uku da biyu. Shahararren dan wasan kwallon Tennis na duniya dan asalin kasar Sabiya Novak Djokovic ya samu nasarar zuwa wasan dab da na kusa da na karshe a gasar Australian Open da ke gudana a yanzu haka a kasar Ostireliya. Mai shekaru 35 a duniya, Djokovic ya samu nasarar kai wa zagayen na quaterfinals ne bayan da ya lallasa abokin karawarsa Alex de Minaur da ci shida da biyu da shida da daya da kuma shida da biyu. Wannan nasara dai, ta bude hanyar sake lashe guda daga cikin manyan wasanni na kwallon Tennis karo na 10 ga Djokovic.