Garambawul ga majalisar ministoci a Nijeriya
October 30, 2008Talla
Da yammacin ranar Laraba 29 ga watan Oktoban shekara ta 2008, shugaban tarayyar Nijeriya Umar Musa ´Yar Adua ya sanar da yiwa majalisar ministocin gawambawul, matakin da aka daɗe ana jiran ya aiwatar a ƙasar ta Nijeriya mai arzikin man fetir. Wannan garambawul na farko da fadar shugaban ƙasa a Aso Rock ta yi ya shafi ministoci 20 na gwamnatin shugaba ´Yar Adua.