Gambiya za ta fice daga kotun duniya | Labarai | DW | 26.10.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gambiya za ta fice daga kotun duniya

Gambiya ta bi sahun kasashen Afirka ta Kudu da Burundi wajen neman fita daga kotun duniya mai hukunta manyan laifukan yaki.

Kasar Gambiya ta zama kasa na baya-baya cikin kasashen Afirka da suka nuna bukatar ficewa daga cikin kotun duniya mai hukuntan manyan laifukan yaki, inda ta zargi kotun da musguna wa 'yan Afirka, kamar yadda ministan shari'a na kasar Sheriff Bojang ya sanar da gidan talabijin na gwamnati. Matakin kasar da ke yankin yamamcin Afirka yana zuwa bayan kasashen Afirka ta Kudu da Burundi sun bayyana matakin watsi da kotun ta duniya cikin wannan wata na Oktoba da muke ciki.

Matakin na Gambiya zai iya shafi kotun mai mazauni a birnin Hague na kasar Holland, saboda babbar mai gabatar da kara a kotun Fatou Bensouda ta kasance 'yar kasar ta Gambiya. Matakin gwamnatin Gambiya ya zo makonni kafin zaben shugaban kasa na ranar daya ga watan Disamba mai zuwa, inda Shugaba Yahya Jameeh yake rike da madafun iko tun shekarar 1994 bayan juyin mulki na sojoji.