1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

G7: Taron gaggawa kan hare haren Rasha

Abdullahi Tanko Bala
October 11, 2022

Shugabannin kungiyar kasashen G7 za su gudanar da taron gaggawa kan sabbin hare haren Rasha a biranen Ukraine da suka hada da birnin Kyiv a karon farko bayan watanni.

https://p.dw.com/p/4I2rM
Olaf Scholz a taron G7
Olaf Scholz a taron G7Hoto: Jens Krick/Flashpic/picture alliance

Sabbin hare haren na Rasha a biranen Ukraine sun haddasa mutuwar akalla mutane 19 yayin da wasu mutanen 105 suka jikkata a cewar jami'an kasar Ukraine.

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz wanda har ila yau yake rike da shugabancin karba karba na kungiyar ta G7 ya tabbatar wa shugaban Ukraine cewa Jamus da sauran kasashen G7 suna tare da Ukraine kuma za su cigaba da taimaka wa kasar.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron yace sabbin hare haren da Rasha ta kai sun nuna gagarumin sauyi a yanayin yadda yakin ke gudana.

Fadar gwamnatin Rasha ta Kremlin tace tana tsammanin karin tsamin dangantaka da kasashen yamma gabanin taron gaggawa na kungiyar kasashe masu karfin tattalin arziki na duniya na duniya G7 inda za su tattauna hare haren baya bayan nan da Rasha ta kai a wasu biranen Ukraine.

Kakakin fadar Kremlin Dmitry Peskov ya shaidawa manema labarai cewa abu ne mai sauki a fahimci inda kungiyar ta sanya a gaba kuma Rasha a shirye ta ke ta cimma manufarta a Ukraine.

Shugaban Ukraine din Volodymyr Zelensky zai bukaci shugabannin kungiyar ta G7 su gaggauta taimaka wa kasarsa da jiragen yaki bayan harin da Rasha ta kai wa kasarsa a baya bayan nan.

A waje guda shugaban Amirka Joe Biden a ranar litinin ya yi wa shugaban Ukraine alkawarin Amirka za ta bai wa kasarsa karin makaman kakkabo jiragen sama bayan harin makamai masu linzami da Rasha ta harba cikin Ukraine.