1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasashen G7 na daukar China a matsayin barazana

Abdoulaye Mamane Amadou
May 4, 2021

Ministocin harkokin wajen kasashen G7 masu karfin tattalin arziki sun cimma matsaya kan batun hada karfi waje daya don tinkarar China, da suka ce ke neman kasance masu barazana.

https://p.dw.com/p/3sxq1
G7-Gipfel in London
Hoto: Stefan Rousseau/AP Photo/picture alliance

A wata hira da manema labarai a gabanin taron kolin kungiyar, babban sakataren harkokin wajen Amirka Antony Blinken, ya bayyana cewa manufar da kasashen suke son cimma ita ce na tilasta wa sauran kasashe amfani da sharudan da duniya ta cimma, ciki har da kasar China da ke barazana ga batun kare 'yancin bani Adama ga masu rajin girka dimukuradiyya a Hong Kong, hakan da ma tsirarrun Musulmai 'yan kabilar ouïghoure Xinjiang.

Rahotanni sun ce ko baya ga taron na ministocin harkokin wajen, a nasu bangare suma ministocin kudi menbobin kungiyar ta G7 za su gabatar da nasu taron daga yau zuwa gobe a birnin Landan.