G7: Agajin kasashen da corona ta galabaita | Labarai | DW | 19.03.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

G7: Agajin kasashen da corona ta galabaita

Ministocin kudi na kasashe masu karfin tattalin arziki na G7 sun kara jaddada matsayinsu na tallafawa kasashe masu raunin tattalin arziki da annobar corona ta yi wa illa.

A yayin taron kolin da suka gabatar a yau din nan ta hanyar bidiyo karkashin jagorancin Birtaniya, ministocin sun ce asusun bada lamuni na duniya IMF ne zai jagoranci bayar da agajin ga kasashen.

A wata sanarwar bayan taron da ministocin suka fitar, kasashen sun ce wazirin Birtaniya Rishi Sunak, da sauran ministocin kudin na G7, na son ganin an kada kuri'a ne tsakanin kasashen da za su ba wa tallafin na tsabar kudi a matsayin taimako.