1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ghana: Fulani sun koka kan nuna musu wariya

June 15, 2021

Al’ummar Fulani sun baiyana damuwa akan nuna masu a tsakanin sauran kabilu a daidai lokacin da hukumar kidayar al’umma da gidaje a Ghana ta fara wani atisayen kidayar jama’ar kasar.

https://p.dw.com/p/3uz6U
Nigreria Fulani-Nomaden
Hoto: AFP/Luis Tato

Alkalluman bincike na nuni da cewar akalla unguwanni 300 ne suka kafu a Ghana tare da gudunmuwar al’ummar Fulani, wanda ya kasance dalili mai karfi da ya sanya shugabannin Fulanin, suka nuna turjiya akan kidaya Fulani a cikin kananan kabilun Ghana a maimakon babbar kabila mai cin gashin kanta. 

Sheikh Ahmed Mohammad Gedel, shi ne daraktar kungiyar kare hakkokin Fulani da tsaro wato African centre for Fulbe Affairs, ya baiyana cewa tun daga shekarar 1948 da’a aka yi irin wannan kidayar, ana sanya Fulani a ciki.

Sheikh Mohammad Gedel, ya yi korafin cewa yanzu wani yunkuri ake yi na kushe gudunmuwar da Fulani ke bayarwa wajen ci gaban kasar Ghana. Farfesa Sheikh Usman Bari, jigo ne a cikin dattawan kasar Ghana kuma mai fada aji, hakzalika mai ruwa da tsaki.

Sai dai shugaban kula da atisayen kididdigar na bana Owusu Kagya yace korafin cewa ana nuna wa Fulani wariya ba gaskiya ba ne domin an shigar da kowa da kowa kuma a bana suna aiki ne tare da shawarwarin tsangayar tantance adadin yaruka a Ghana wajen wanzar da ayyuka domin su ne kwararru wajen lissafa harsuna da kabilu.

Abin jira a gani dai shi ne cewar ko koken da kungiyar Fulanin ta ACFA ta gabatar wa hukumar kula da kididdigar bayanan 'yan kasa zai yi tasiri ko akasin haka.