1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tarihi

Flora Nwapa: Jagorar adabin zamani na Afirka

Sam Olukoya ATB/MNA
October 1, 2020

'Yar Najeriya mawallafiya Flora Nwapa, littafinta Efuru ya sa ta zama mace ta farko da ta wallafa littafi da turanci. Aikinta ya share fage ga baiyanar mata mawallafa a Najeriya da sauran kasashen Afirka.

https://p.dw.com/p/3jEQb
Projekt African Roots

Yaushe Flora Nwapa ta rayu?

An haifi Flora Nwapa a watan Janairu 1931 a Oguta, jihar Imo, a Gabashin Najeriya. Ta fara karatunta a Oguta da Fatakwal da kuma Legas. Ta yi makarantar kwalejin jami'ar Ibadan a Najeriya da jami'ar Edinburgh a Birtaniya. Nwapa ta rasu a watan Oktoba 1993 sakamakon ciwon pneumonia (nimoniya) tana da shekaru 62.

Mene ne taken littattafan Flora Nwapa?

Ta hanyar littattafanta, Flora Nwapa ta yi kokarin sauya labaran maza marubuta na Afirka wadanda rubuce-rubucensu ke cike da sabanin tunani kan matan Afirka. Littattafan Nwapa sun baiyanar da akasin haka, inda ta rika ba da labarai na nasarori da matan Afirka suka samu. Littattafanta kamar Efuru da Idu sun kalubalanci al'adar yadda ake baiyana matan Afirka a matsayin wadanda dole a ko da yaushe su kasance karkashin inuwar maza saboda ana daukar mace a matsayin ya kamata ta bi, ta mika wuya kuma wacce ba ta da wani amfani.

Wadanne ne mashahuran littattafan Flora Nwapa?

Daya daga cikin littattafan Flora Nwapa da suka shahara shi ne Efuru. Littafin ya baiyana rayuwar wata mata wacce ta nuna karfin hali da karfin zuciya har ma da taimaka wa mijinta da mahaifinta da kudade. Efuru, tauraron labarin littafin ya sauya tunanin mayar da mata baya da ake nunawa a zamantakewar al'adar gargajiya ta al'ummar Afrika, inda ta nuna nata ra'ayin na dabam.

Flora Nwapa: Jagorar adabin zamani na Afirka

Ta zartar da wasu kudurori muhimmai a rayuwarta bisa abin da take gani ya dace da ita maimakon mika wuya ga bukatun al'adun gargajiya na Afirka. Sauran littattafai da ta wallafa sun hada da Idu da Never Again da One Is Enough da kuma Women Are Different.

Me aka gada daga Flora Nwapa? 

Watakila babban abin da za a tuna ta da shi, shi ne samar da mata marubuta wadanda suke maimaita jigon littattafanta a wani yunkuri na sauya labarai marasa dadi game da matan Afirka a yanayin da maza suka kankane fagen adabi.

Shin Flora Nwapa 'yar fafutukar ganin daidaiton jinsi ce?

Yayin da Flora Nwapa ba ta daukar kanta a matsayin mai gwarwarmayar daidaiton jinsi, wasu daga cikin littattafanta sun shahara wajen kare hakkin mata. A rubuce-rubucenta tana amfani da sunayen mata wajen kalubalantar al'adu na rashin adalci ga mata wanda har yanzu yake karfafa gwiwar mata 'yan fafutuka.

Shawarwarin gina wannan labarin sun samu ne daga masanan tarihi Farfesa Doulaye Konaté, Lily Mafela, Ph.D., da Farfesa Christopher Ogbogbo. Shirin African Roots ko Tushen Afirka na samun tallafi daga Gidauniyar Gerda Henkel.