1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Fiye da dalibai 100 aka sace daga makarantar Islamiyya

Ramatu Garba Baba
May 31, 2021

Al'ummar garin Tegina sun fada cikin damuwa bayan sace daliban makarantar Islamiyya a yayin da mahukunta ke kokarin ganin an 'yanto daliban daga hannun 'yan bindiga.

https://p.dw.com/p/3uClT
Nigeria Abuja | Proteste | Entführte Studenten
Hoto: Kola Sulaimon/AFP/Getty Images

Maharan sun afaka cikin garin na Tegina ne a kan babura dauke da manyan bindigogi inda suka rinka harbe-harbe da ya kidima daukacin alummar garin, kafin suka yi wa makarantar ta Islamiyyar diran mikiya inda suka kwashe daliban. Rundunar ‘yan sandan jihar ta Neja, ta ce har yanzu ba su tantance adadin yaran da aka kwashe ba. Yayin da gwamnatin jihar ke bayyana takaicin sake fuskantar sace daliban makaranta.


Rahotani sun bayyana cewa 'yan bindigar sun bar wasu daliban saboda yara kanana ne da ba su iya tafiya sosai ba. Tuni dai gamaiyyar kungiyoyin farar hula na yankin arewacin Najeriya suka maida murtani a kan lamarin da suka bayyana shi da mai tada hankali. Yayin 

Yawan sace daliban makaranta dai sannu a hankali ya zama ruwan dare, domin koda a watan Febrairun da ya gabata, sai da aka sace dalibai da malamai kimanin arba'in da daya a makarantar Sakandaren Kagara da ke jihar ta Neja, abinda ke nuna tabarbarewar yanayin tsaron da gwamnati ke cewa tana daukan matakin shawo kansa.