Fitattun 'yan wasa a gasar cin kofin duniya ta mata
Wadanne ‘yan wasa ne za su kafa tarihi a gasar kofin duniya ta mata? Wacce ce za ta yi zarra a karshe? Akwai dai hazikai daga cikinsu. ga wasu 12 DW ta zabo wadanda ake iya sa ido.
Lieke Martens ('Yar kasar Holland)
Tauraruwar kasar Netherlands, ta ci gasar kasashen Turai shekaru biyu da suka gabata. Tuni ma Martens daga cikin fitattun 'yan wasa a duniya. 'Yar shekaru 26 da ke yi wa Barcelona wasa, ana yi mata lakabi da kanwar 'Messi' saboda salonta na taka leda. Kwararriya ce matuka wajen sarrafa kwallo da kuma ci. A shekara ta 2017, ta kasance 'yar wasan da hukumar FIFA ta karrama a matsayin zakakura.
Christine Sinclair ('Yar kasar Kanada)
Wannan gwana wacce ta fi cin kwallaye, za ta buga wasanta a gasar ne karo na biyar yanzu a Faransa. Duk da kasancewarta mai shekaru 36, har yanzu Sinclair, na da muhimmanci ga kungiyar kwallo ta kasarta. Tun fara wasa a shekarunta na haihuwa 19, sau 282 ta taka leda a wasannin da ta ci wa Kanadar kwallaye har sau 181.
Wendie Renard ('Yar Faransa)
Wendie Renard, fitacciya ce a wasan tsakiya, ta kuma ci gasar Lik-Lik na Faransa har sau 13 a jere da kuma gasar zakarun Turai sau shida. Renard har ila yau, ta kware a fannin tsare baya a tsakanin takwarorinta na duniya, a ganin za ta taka rawar gani a kokarin da Fransa ke yi na ganin ta dauki kofin na duniya rukunin na mata ta bana.
Lucy Bronze ('Yar Ingila)
Lucy Bronze, daya ce daga cikin fitattun mata 'yan kwallo a duniya, ko tantama babu ita ce babbar 'Yar wasa a kungiyarta a gasar ta Faransa. Bronze, ta karbi lambobin yabo a matakan kungiya lokuta da dama. A gasar shekara ta 2015, ta zo ta uku, kuma ta je wasan kusa karshe a wasannin kasashen Turai a sheakara ta 2017. A bana ta jajirce don ganin ta ninka abin da ta yi a baya.
Irene Paredes ('Yar kasar Spain)
Mai kuzari da gudun tsiya, Paredes, kanwa ce uwar gami kuma abar misali. 'Yar wasan tsakiya wadda ta yi wa Paris Saint-Germain wasa a shekarar 2016, ta kuma kware a fannin kai farmaki. Paredes, ta ci wa Spain kwallaye hudu lokacin fafatawar neman cancantar gasar duniya abin da ya dora ta a saman teburi. Irene Paredes, mai tsaron baya ce da za ta fuskanci Jamus a wasannin rukuni-rukuni a Faransar.
Marta ('Yar kasar Brazil)
"Mace kamar maza'' Sau shida Marta Vieira da Silva mai shekaru 33 ke zama gwarzuwar shekara ta hukumar FIFA rukunin mata. Ana ganin cewa har yanzu za ta ci gaba da rike wannan kambu nata. Ba dai shakka ga mutane da dama, Marta za ta ci gaba da zama gwana ta gwanaye a bangaren na mata a duniyar kwallon kafa.
Carli Lloyd ('Yan kasar Amirka)
Wannan 'yar wasan tsakiyar ita ce ta ci wa Amirka kwallayen da suka bai wa kasar lambar zinare a shekarun 2008 da kuma 2012 a wasannin Olympics. A gasar kuma ta duniya a shekara ta 2015, ta ci a fafatawa tsakanin Amirka da Japan da aka tashi 5-2. Haka nan a shekarun 2015 da 2016 ta kasance wacce ta fi fice a cewar hukumar kwallo ta duniya FIFA.
Asisat Oshoala ('Yar Najeriya)
Baiwar Oshoala, ta fito fili ne a shekarar 2014 lokacin gasar kofin duniya na 'yan kasa da shekaru 20. Duk da ya ke Najeriya ba ta dauki kofi a shekarar ba, Oshoala ta ci kwallaye bakwai da suka ba ta kyautar kwallo da takalman zinare. Yanzu likafarta ta yi gaba, saboda tana yi wa kungiyar Barcelona wasa. Sau uku Asisat ta ci gasar kasashen Afirka ta mata.
Dzsenifer Marozsan ('Yar kasar Jamus)
Lamba 10 ta Jamus, hazika ce gwanar taka leda. Bata da ta biyu a fannin kai kwallo raga. Marozsan na daga cikin wadanda suka yi fice a fannin karbar lambobin yabo a fagen wasa a Jamus. 'Yar shekara 27, ta kuma ci gasar zakarun Turai har sau hudu. A 2013 ma ta ci gasar kasashen Turai, sannan shekaru uku daga bisani da sami zinare a gasar Olympics. Yanzu ta shirya sama wa Jamus nasara a Faransar.
Amandine Henry (Faransa)
Amandine Henry (daga dama), wata kwararriya ce a fagen iya kwace kwallo kuma ta yi zarra wajen sarrafa ta daga kowane bangare. Yadda matashiyar mai shekaru 29 ke kallon gasar wannan karo da za abuga a Faransa, za ta kasance dalilin shigarta cikin gwanayen mata a fagen tamaula a duniya.
Samantha Kerr ('Yar kasar Ostireliya)
Samantha Kerr, na rike da kambun kwallaye 50 na musamman da aka ci a gasar Lik-Lik ta mata a Amirka. Tun tana 'yar shekara 15 da haihuwa ta fara wasa a kungiyar kwallo ta kasarta. Kungiyarta ta zama ta shida a jerin kasashen da FIFA ta jera a gasar Faransa ta bana. Da irin wannan salon da ake gani ta ke nuna murna a duk lokacin da ta ci kwallo, salon da masoyanta ke son gani sosai.
Saki Kumagai (Japan)
Kumagai ta ci wasannin Lik-Lik na Faransa sau shida daban-daban da kuma Olympique Lyon. haka kuma ta sau hudu tana cin kofi a gasar zakarun Turai. Keftin din Japan, ta kai kasarta ga nasara a gasar kasashen Asiya a 2018. An nada Kumagai matsayin keftin a 2018, bayan rike matsayin tun a 2011 bayan nasarar Japan kan Amirka a bugun Fenariti da ta ci. Lambobi sama da 100 ta sama wa Japan.