Fitattun ′yan siyasa suka halarci bikin cikar Cocin Evangelika shekaru 500 | Zamantakewa | DW | 30.05.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Fitattun 'yan siyasa suka halarci bikin cikar Cocin Evangelika shekaru 500

Taron da ya gudana a birnin Berlin na Jamus, a wannan karo kwararrar 'yan siyasa da a bikin da sauye-sauye da aka samu a cocin wanda Martin Luther ya jagoranta sun kara wa bikin armashi. 

Kwanaki biyar aka kwashe ana gudanar da taro, inda majami'u da ke birnin na Berlin fadar gwamnatin Jamus suka cika suka batse. Wani abu da ya kara wa bikin na bana armashi na zaman dandazon 'yan siyasa wajen bikin na coci da suka hada da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, da shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier, da ministan harkokin waje Sigmar Gabriel, da ministan harkokin cikin gida Thomas de Maiziere, da ministan kudi Wolfgang Schäuble. Shi ma babban dan takara adawa Martin Schlulz na jam'iyyar SPD wajen neman shugaban gwamnatin ya halarci zauren taro, haka tsohon shugaban kasar Amirka Barack Obama.

Ga ma dai abin da Christina Aus, shugabar shirya wannan taro ta bayyanan cewa a ganinta haka ake bukata: "Ina tsammani coci da siyasa suna tafiya kafada da kafada, kuma saboda haka wannan lokaci ne da ya hada 'yan siyasa daga bangarori daban-daban.  Duniya tana cikin wani hali amma haka ya nuna za a iya aiki da zuciya daya wajen cimma buri."

Wannan babban taro na Kirstoci 'yan Evangelika ya kuma nuna muhimmancin aiki tare tsakanin mabambantan ra'ayoyi, domin samar da mafita game da ricike-rikice da sabanin da ke tsakanin mutane.

Inda Christina Aus ta nuna muhimmancin fahimtar juna tsakanin mabiya addinai daban-daban: "Babu yadda za a yi addinai su kauce wa juna a wannan duniya da take dunkulewa, amma ba mu da masaniya sossai game da juna. Wannan rana ta coci tana bukatar gina gada tsakanin Kiristoci da Musulmai".

A cikin manyan malaman Musulunci da aka gayyata wajen taron akwai Sheikh Ahmad al-Tayyeb limanin Jami'ar al-Azhar da ke birnin Alkahira na Masar, wanda ya yi muhawara tare da ministan cikin gidan Jamus Thomas de Maiziere kan nuna sanin ya kamata.

Wani abu da shugabar shirya taron Christina Aus ta yaba da shi, na zaman matakan tsaro kadaran-kadahan da aka dauka: "Wannan rana ce kuma ta dakile tsoro. Mun ji dadin yadda muka yi komai cikin kwanciyar hankali. Babu wanda ya yi mana barazana yayin da muka hadu. Akwai matakan tsaro, amma ba mu kasance kewaye da katanga ba."

Fiye da mutane 100,000 suka halarci wannan taro na Kiristoci da ya gunada tsakanin birnin na Berlin fadar gwamnatin Jamus da kuma garin Wittenberg.