Firaministan Turkiya ya goyi da bayan ɗage hanin ɗaura ɗan kwali a jami´o´i | Labarai | DW | 19.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Firaministan Turkiya ya goyi da bayan ɗage hanin ɗaura ɗan kwali a jami´o´i

FM Turkiya Rejep Tayyip Erdogan ya ce yana son a dage haramcin sanya dan kwali ga mata a jami´o´in kasar baki daya. FM na Turkiya ya fadawa jaridar Financial Times cewa bai kamata a kayyade ´yancin samun ilimi mai zurfi ga mata saboda tufafi da suke sanyawa. Shi ma shugaban kasar ta Turkiya Abdullah Gül ya furta irin wadannan kalamai. A dai halin da ake ciki gwamnatin jam´iyar AKP mai ra´ayin mazan jiya ta na aikin fasalta sabon kundin tsarin mulkin kasar. To sai dai ba´a sani ba ko za´a tabo batun dage haramcin sanya dan kwalin a jami´o´in kasar. Hana daura dan kwali a ma´aikatun gwamnati da jami´o´i a Turkiya ya samo asali ne sakamakon wani juyin mulkin soji a shekara ta 1980.