1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Firaministan Isra'ila ya yi ikirarin lashe zabe

March 24, 2021

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, ya yi ikirarin lashe zaben 'yan majalisar dokokin kasar da aka yi a ranar Talata, zabe na hudu cikin shekaru biyu saboda rigingimu.

https://p.dw.com/p/3r2BN
Israel Parlamentswahl  | Wahlsieger Netanjahu
Hoto: Noam Moskowitz/dpa/picture alliance

Firaminista Benjamin Netanyahu, wanda ya fi kowa dadewa a wannan matsayi a tarihin Isra'ila, ya yi fatan zaben zai ba shi damar kafa gwamnati ba tare da wata hadakar ba, abin da ake ganin da wuya ne ya cimma hakan.

Kuri'ar jin ra'ayi dai ta nuna yiwuwar jami'iyyar Mr. Netanyahun ta samu 'yar galaba a majalisar.

Cikin watan Disambar bara ne gwamnatin ta wargaje sakamakon rashin jituwa tsakanin Mr. Netanyahu da madugun adawa Benny Gantz da suka yi hadin gwiwa wajen kafa ta.

Firaminista Netanyahu wanda ke fama da zarge-zarge ciki har da na cin hanci, ya yi tutiyar cin zaben saboda kokarin da ya yi a bangaren yaki da cutar corona.