Firaministan Iraki ya kai ziyara Ramadi | Labarai | DW | 29.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Firaministan Iraki ya kai ziyara Ramadi

A wani mataki na jinjinawa dakarun sojojin da suka yi ayyukan kwato birnin Ramadi daga hannun mayakan kungiyar IS, Haidar al-Abadi ya kai ziyara birnin na Ramadi.

Firaministan Iraki Haïdar Al-Abadi ya kai wata ziyara a wannan Talatar a birnin Ramadi da ke yammacin Bagadaza bayan da dakarun sojan kasar suka tabbatar da kwace shi daga hannun mayakan kungiyar IS da suke rike da birnin tun daga watan Mayun da ya gabata.

Shugaban gwamnatin ta Iraki dai ya isa ne ta wani jirgi sama mai saukar ungulu tare da rakiyar wani babban sojan kasar inda suka sauka a wata jami'a da ke Kudancin birnin. Firaministan zai samu ganawa da jagoran sojojin da suka kai farmakin kwato birni na Ramadi da kuma na rundunar yaki da ta'addanci ta kasar.

Wannan dai wata babbar nasara ce ga gwamnatin kasar ta Iraki, inda Firaministan da kanshi ya sanar da wannan ziyara ta shi ta shafinsa na Twitter.