Firaiminista Modi ya lashe zaben Indiya | Labarai | DW | 23.05.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Firaiminista Modi ya lashe zaben Indiya

Hukumar zaben kasar Indiya ta nuna jam'iyyar BJP mai mulki a kasar na kan gaba da yawan kujeru 299 cikin kujeru 542 da ake da su a majalisar dokokin kasar, yayin da babbar jam'iyyar adawa ke da kujeru 50.

A wani sabon babin shugabancin wa'adi biyar nan gaba, firaiministan Indiya Narendra Modi ya samu nasara a zaben kasar mafi girma da tasiri a tarihin siyasar duniya. Shugaban babbar jam'iyyar adawa ta INC Rahul Ghandhi ya amince da shan kaye a zaben, Shuga Donald Trump na Amirka da firaiministan kasar Pakistan na cikin shugabannin duniya da suka taya Narendra Modi murnan lashe zabe.

Akalla mutane miliyan 600 ne aka kiyasta suka kada kuri'a a zaben na Indiya, sai dai ana ganin samar da ayyukan yi tsakanin al'ummar kasar da sasanta rikici tsakanin Pakistan da Indiya na cikin manyan jan aikin da ke gaba firaiminsita Modi a sabon wa'adin shekaru biyar da zai yi.