Ficewar Birtaniya tana kasa tana dabo
October 18, 2018Talla
Jagororin na Turai sun ce babu wani abin kwarai da aka cimma a kan wannan batu, wanda zai kai su ga wani muhimmin taron koli cikin watan gobe na Nuwamba.
Firaministar Birtaniya Theresa May, yayin wani jawabin da ta yi a gaban takwarorinta a jiya Laraba, ta ce lamarin na bukatar jajircewa kafin a cimma yarjejeniyar.
Babban mai shiga tsakani a kungiyar, Michel Barnier, ya yaba kwazon bangarorin da ke fadi tashi kan wannan yarjejeniya, sai dai ya ce ba a kaiga samun abin da ake bukata ba.
Tun da fari dai shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, ta gargadi kungiyar kan yiyuwar a karshe Birtaniyar ta fice ba tare da an cimma wata yarjejeniyar ba.