Fargabar yiwuwar ambaliya a Najeriya | Labarai | DW | 06.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Fargabar yiwuwar ambaliya a Najeriya

Kamaru ta sanar da cewa za a sako ruwan Lagdo Dam da ke a Arewacin na Kamaru inda ruwan zai ci gaba da biyo kogin Benue da ke a Najeriya.

Flut Nigeria Afrika 2010

Al'umma da fargabar tumbatsar koguna

Mahukunta a Najeriya sun bukaci dubban mutane da ke zaune a kusa da gabar kogi su shirya kauracewa muhallansu saboda fargabar ambaliyar ruwa, bayan da mahukuntan a kasar Kamaru suka ce zasu sako ruwa saboda cikar madatsun ruwansu.

Hukumar agajin gaggawa a Najeriyar NEMA ta bayyana haka inda ta ce mahukuntan na kasar Kamaru sun sanar da su cewa za a sako ruwa sannu a hanakali daga madatsar ruwa ta Lagdo da ke a Arewacin na Kamaru inda ruwan zai ci gaba da biyo kogin Benue har zuwa watan Nuwamba.

Sako ruwa daga wannan dam na Kamaru dama ruwan sama da aka fiskanta mai karfin gaske a shekarar 2012 ya haifar da mummunar ambaliyar ruwa a Gabashi da Tsakiyar kasar ta Najeriya. Lamarin da ya jawo rasa rayuka da dukiyoyin al'umma da sanya sama da mutane 120,000 suka kauracewa muhallinsu.