1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gaza: Fargabar dakatar da agajin jin-kai

Lateefa Mustapha Ja'afar
October 24, 2023

Hukumar Majalisar Dinkin Duniya da ke Kula da 'Yan Gudun Hijirar Falasdinu UNRWA, ta bayyana cewa akwai yiwuwar tilas ta dakatar da ayyukanta na jin-kai a yankin Zirin Gaza na Falasdinun.

https://p.dw.com/p/4XzBI
Falasdinu | Zirin Gaza | Rafah | Man Fetur | Agaji | Majalisar Dinkin Duniya
Akwai bukatar gaggauta agajin man fetur zuwa Zirin GazaHoto: Mohammed Abed/AFP/Getty Images

Hukumar Majalisar Dinkin Duniyar da ke Kula da 'Yan Gudun Hijirar Falasdinun UNRWA ta ce, matakin dakatar da aikin a yankin Zirin Gazan ya zama wajibi in har ba su samu man fetur ba. Da take jawabi ga kamfanin dillancin labaran Jamus dpa, daraktar hukumar Juliette Touma ta ce ba za su iya ci gaba da kai tallafi ga al'ummar Zirin Gaza da ke cikin tsananin bukatar kayan agajin jin-kai ba ina har ba su samu man fetur din ba. A cewarta 'yan gudun hijirar Falasdinu da yawansu ya kai dubu 600 na warwatse a sansanonin UNRWA sama da 150, kuma dukkancu sun dogara ne kacokam ga tallafin hukumar.