1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fargabar ambaliya a wasu sassan Najeriya

May 18, 2018

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya wato Nigeria Hydrological Services Agency a Turance ta sanar da cewa kimanin jihohin kasar 35 ke fiskantar barazanar ambaliya.

https://p.dw.com/p/2xxxS
Überschwemmung in Nigeria
Hoto: Getty Images/AFP/P. Utomi Ekpei

Yayin da damuna ta bana ke fara kankama masana da masharhanta sun fara tofa albarkacin bakinsu kan matakai da ya kamata a dauka don magance barnar da ambaliyan ka iya haifarwa.

Matsalar ambaliyan ruwa dai ta zama ruwan dare gama Tarayyar Najeriya inda kusan kowace shekara da damuna ta kama ake fama da ita a kusan dukkanin jihohin kasar har ma da Abuja.

Hukumomi dai na cewa suna iya kokari wajen ganin an magance matsalar to amma saboda yadda ake zargin mutane sun jahilci muhimmancin kare muhalli da kuma rashin dokoki masu tsauri da za a hukunta masu gurbata muhalli wannan matsala na ci gaba da wanzuwa.

Überschwemmung in Nigeria
Hoto: Getty Images/AFP/P. Utomi Ekpei

Kamar kowace shekara a bana ma hukumar kula da yanayi ta Najeriya wato Nigeria Hydrological Services Agency a Turance ta sanar da cewa kimanin jihohin kasar 35 ake hasashen za a samu ambaliyar ruwa a wannan damuna ta bana.

Masana muhalli sun nemi hukumomi su dauki tsauraran matakai na bude hanyoyin ruwa da kuma karfafa wasu dokoki da za su kare muhalli ko a rage irin barnar da ambaliyar ruwa ka iya yi.

Kamar irin jihohin Yobe ita ma jihar Borno ba a bar ta a baya ba wajen daukar matakan magance matsalar muhallin da ma matsalar gurgusowar hamada kamar yadda Hon. Kaka Shehu kwamishinan shari'a da kuma kula da ma'aikatar muhalli a jihar Borno ya tabbatar.

Überschwemmung in Nigeria
Hoto: picture alliance/AA/S. Adelakun

To sai dai dukkanin wadannan matakai ba za su samar da nasarar da ake bukata ba sai su ma al'umma sun ba da ta su gudunmawa kamar yadda Abdullahi Bego daraktan yada labarai na gwamnatin jihar Yobe ya bayyana.

Masana dai sun ce akwai bukatar ci gaba da ilimantar da al'umma kan muhimmancin kare muhalli, hakan zai tamaka wajen rage matsalar dumamar yanayi da ma na ambaliyan ruwa.