1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fargaba a Borno kan musayar 'yan Chibok

May 8, 2017

Gwamnatin jihar Borno ta yi tsokaci kan musayar 'yan matan Chibok 82 da wasu manyan mayakan Boko Haram yayin da al'umomin Arewa maso gabashin Najeriya ke bayyana fargabar sako kwamandojin.

https://p.dw.com/p/2cca5
Nigeria Präsident Muhammadu Buhari und die freigelassenen Chibok-Mädchen in Abuja
Shugaban Najeriya lokacin da ya karbi 'yan matan Chibok 82 da aka sallamo.Hoto: Reuters/Presidential Office/B. Omoboriowo

Wasu sun yaba wa gwamnati saboda samun nasarar ceto 'yan matan da rayukansu bayan kwashe shekaru uku a hannun mayakan na Boko Haram, inda wasu ke nuna damuwa kan hanyoyin da aka bi wajen sakin 'yan mata wanda suka ce abin tsoro ne. Da take bayar da na ta martanin gwamnatin jihar Borno ta ce samun nasarar ceto 'yan matan abin farin ciki ne da jin dadi kuma hakan na tabbatar gaskiya da tsayuwar daka da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ke yi a shiyyar Arewa maso gabashin Najeriya.

Farin ciki gami da shakku a Arewa maso Gabashin Najeriya
Gwamnan jihar Borno Kashim Shetima ya ce sako 'yan matan ya fitar da gwamnatin jihar daga zargin da a baya aka mata na cewa sun boye 'yan matan ne inda kuma ya bayyana kwarin gwiwar cewa nan kusa sauran 'yan matan ma za su dawo ga iyayensu. Sai dai wasu al'ummar shiyyar Arewa maso gabashin Najeriya sun bayyana damuwa kan musayar kwamandojin na Boko Haram da 'yan matan wanda suke ganin an karfafa Kungiyar ne ta yadda za su ci gaba da halaka fararen hula kaman yanda Malam Bulama Mafa wani mazaunin Maiduguri ya yi tsokaci:

Kashim Shettima Gouverneur Bono Nigeria
Gwamnan jihar Borno Kashim ShettimaHoto: DW/U. Shehu

"Abin tsoron shi ne ba a san su waye kwamandojin Boko Haram din da aka sake a wannan yarjejeniya ba kuma ba a san sake su abin da zai haifar wa zaman lafiya da aka samu ba."

Wasu 'yan Najeriya na fatan ganin an sako na su 'ya'yan
Wasu da suka ce Kungiyar Boko Haram ta sace musu 'ya 'yansu wadanda ba a maganarsu kaman yadda ake yi kan 'ya Chibok sun nemi gwamnati da ta fadada wannan kokari na ta domin a gano musu nasu 'ya 'yan dan samun kwanciyar hankali. Pastor Joseph na kauyen Pelechiroma a karamar hukumar Hauwl a jihar Borno ya mika kuka a madadin wadan nan iyaye.

Warten auf die verlorene Tochter
Wasu iyayan da rikicin Boko Haram ya batar da 'yar suHoto: DW/T.Mösch

" Muma muna roko a tuna da mu a share mana hawaye domin kullum muna cikin bakin ciki, muna kuka saboda bakin cikin sace 'ya 'yanmu. Muna roko ga gwamnatin tarayya ta tuna da mu muma a share mana hawaye a dawo mana da 'ya 'yanmu da aka sace ba tare da sanin gwamnati ba."

Wannan ma kuma shi ne irin kukan da yawancin iyaye da aka sace musu 'ya 'ya ke yi wanda kuma sun kai dubbai, amma babu wanda yake fafutuka a madadin su kamar yadda aka maida hankali kan 'yan matan Chibok.