Farautar wani ɗan bindiga a birnin Paris | Labarai | DW | 18.11.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Farautar wani ɗan bindiga a birnin Paris

'Yan sandan Faransa sun ce suna farautar wani ɗan bindiga da ya buɗe wuta a ofishin jaridar Liberation da titin Champs-Elysees da hedikwatar bankin Societe Generale da ke Paris.

Jami'an 'yan sanda a birnin Paris na ƙasar Faransa sun ce suna ci gaba da farautar wani ɗan bindiga da ya buɗe wuta a harabar ofishin jaridar Liberation har ya kai ga ranauta wani ma'aikaci, baya kuma ga jerin wasu harbe-harbe da ya yi a kan titin nan na Champs-Elysees da ya shahara a birnin da kuma gaban hedikwatar bankin Societe Generale. Babban mai gabatar da ƙara na Faransa Francois Molins ya ce suna kyautata zaton mutum guda ne ya tafka wannan ɗanyen aikin a waɗannan wurare, bayan da ya nuna wa manema labarai wani hoton bidiyo da suka samu wanda ke ɗauke da mutumin sanye da bakar taguwa da koren takalmi da kuma hula a kansa.

Ya zuwa yanzu dai hukumomin na Faransa sun ce ba su san dalilin da ya sanya wannan mutumin yin wannan aika-aika ba wadda ke zuwa kwanaki uku bayan da wani mutum shi ma ɗauke da bindiga ya yi barazanar hallaka wasu ma'aikatan gidan talabijin din BFM-TV da ke Paris ɗin, kafin daga bisani ya tsere.Tuni dai gidajen watsa labarai na ƙasar da ma ƙungiyar nan ta kare hakkin 'yan jaridu ta Repoters Without Boders suka fara nuna damuwarsu dangane da wannan lamari, tare da yin Allah wadai da shi.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Abdourahamane Hassane