Farashin shinkafa zai haura a Najeriya | Zamantakewa | DW | 14.09.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Farashin shinkafa zai haura a Najeriya

Ma’aikatar noma ta Najeriya ta yi gargadin cewar idan ba a dauki matakai na bunkasa harkan noma ba,to fa kafin nan karshen wannan shekarar to 2016 ,yan Najeriya za su rika sayan buhun shinkafa a farashin Naira 40,000.

A wani taron kwana daya ne karamin ministan noma tare da ci-gaban karkara Najeriya Heineken Lokpobiri ya bayyana cewar Najeriya na kashe kimanin dala biliyan 22 a kowace skekara wajan shigo da abinci daga kasashen wajen,kuma wannan shi ne ya janyo tashin gwauran zabi na kayyayakin abinci a cikin kasuwanin kasar.Inda yake jaddada cewar matukar dai manoman Najeriya suka gaza kawo kayayyakin abincin daga kasashen ketare,to fa kamin nan zuwa karshen wannan shekarar,sai ‘yan Najeriyar za su koma sayan buhun shinkafa Naira 40,000.

Dangane da fargaban da al'umman kasar za su fada cikin tuni dai dattawa suka fara janyo hankalin hukomomi a kan daukar matakan kare al'umma fadawa cikin matsalar yunwa.Karamin minsitan Najeriyar dai ya kara nuni da cewar ana tsamanin cewar a shekara ta 2050,yawan al'umman Najeriyar zai kai miliyan 450 don haka akwai bukatar a kara mayar da hankali ga harkar noman.