Faransawa na tunawa da harin Paris | Labarai | DW | 13.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Faransawa na tunawa da harin Paris

Iyalai da 'yan uwan wadanda suka rasa makusantansu a harin da aka kai mai muni a kasar Faransa sun tsaya tare da Shugaba Emmanuel Macron don bikin tunawa da 'yan uwansu 130 da aka kashe.

An dai tsaurara matakan tsaro yayin wannan biki na jimami da ya sauya makomar kasar ta fiskar tsaro tun bayan harin 13 ga watan Nuwamba shekarar 2015. Ba a dai samu mutane da yawa da aka tsammata ba da suka fita bikin wannan juyayi.

A wajen filin wasa na kasa Stade de France, Macron da mukarrabai da suka rufa masa baya sun ajiye furanni don tunawa da mutum na farko da ya fara halaka a harin , yayin da a sauran wurare da aka kai hare-hare da suka hada da wani wajen shan cafe a birnin na Paris inda aka halaka mutane 29. Akwai kuma iyalai da dama da suka hadu a gaban ginin wajen rawa na Bataclan domin tunawa da 'yan uwansu.