Faransa za ta karfafa yaki da ta′addanci | Labarai | DW | 29.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Faransa za ta karfafa yaki da ta'addanci

A sakamakon jerin hare-hare da ta fuskanta a birnin Paris a watannin baya, Faransa za ta kara kasafin kudin yaki da barazanar ta'addanci.

Gwamnatin Faransa ta ba da sanawar karfafa aikin sojojin ta a wani mataki na dakile barazanar da take fuskanta daga 'yan ta'adda a ciki da wajen kasar. Shugaban Faransa Francois Hollande ya ce a cikin shekaru hudu masu zuwa farawa daga shekarar 2016, za a yi wa ma'aikatar tsaron kasar karin kasafi na Euro miliyan dubu 3.8. Bugu da kari shugaban ya yanke kudurin girke karin sojoji 7000 don yaki da ta'addanci a cikin gida. Tun bayan jerin hare-haren da aka kai a birnin Paris a cikin watan Janeru, Faransar ta kara tsaurara matakan tsaro da yawan dakarun sintiri a fadin kasar baki daya.