1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa: Valls zai nemi shugabacin kasa

Salissou Boukari
December 6, 2016

Da yammacin ranar Litinin ce, Firaministan kasar Faransa Manuel Valls, ya sanar da aniyarsa ta tsayawa takarar neman shugabancin kasar a zabe mai zuwa na 2017.

https://p.dw.com/p/2TnfE
Manuel Valls
Hoto: picture-alliance/AP Photo/T. Camus

Manuel Valls ya ce "kwarai kuwa zan yi takara a zabe mai zuwa na 2017." Firaministan wanda ya sanar a jiyan cewa zai mika takardan murabus dinsa a ranar Talata ga shugaban kasa Francois Hollande,  ya ce ya tsaya takara ne domin dinke barakar da ke cikin jam'iyyarsa tare da neman cigaba da ayyukan da suka faro ta hanyar inganta su da kuma samar wa kasar ta Faransa irin karfin da ta ke da shi na fada a ji a duniya.

A ranakun 22 ga watan nan na Disamba ne dai da kuma 29 ga watan Janairu, 'yan jam'iyyar ta Socialist za su yi na su zaben fidda gwani inda Firaminista Valls zai fafata da wasu kusoshin jam'iyyar kamar su tsohon ministan kudin kasar Arnaud Montebourg da shi ma ke da burin zama shugaban na Faransa.

Wani sakamakon binciken jin ra'ayin jama'a da aka wallafa a ranar Lahadi ya ce Valls dan shekaru 54 da haihuwa zai fi samun amincewar 'yan jam'iyyar domin tsayawa takara a zaben mai zuwa sai dai babban kalubalen da ke gabansa shi ne na dinke baraka tsakanin 'yan jam'iyyar.