Faransa ta nemi shigowar kungiyar NATO don yaki a yankin Sahel | Labarai | DW | 28.11.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Faransa ta nemi shigowar kungiyar NATO don yaki a yankin Sahel

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya yi kira ga aminan kasarsa da su shiga yakin da ake yi da mayakan jihadi da ke hana zaman lafiya a yankin Sahel.

Emmanuel Macron ya fadi hakan ne yayin ganawar da suka yi da shugaban kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg a birnin Paris, inda ya ce yin hakan zai yi matukar tasiri ga dakile ayyukan na ta'addanci. Shugaban na Faransa ya kuma nemi batun ya kasance daya daga cikin manyan batutuwan da kungiyar za ta tattauna a babban taronta da za a gudanar a birnin Landon na Birtaniya nan gaba kadan.