1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jigon IS a Mali ya shiga hannu

Abdul-raheem Hassan
June 15, 2022

Rundunar sojin Faransa a Mali ta sanar da kama wani babban jigo da ake alaka da kungiyar IS a yankin Sahel, Oumeya Ould Albakaye ya shiga hannu bayan shafe tsawon lokaci ana farautarsa.

https://p.dw.com/p/4Cky7
Mali | Sojoji
Hoto: Thomas Coex/AFP

Ma'aikatar tsaron Faransa ta ce an dauki tsawon makonni ana shirya wannan sumame a kusa da iyaka da Nijar, kafin a kama Oumeya Ould Albakaye. Kamen na zuwa ne a dai-dai lokacin da Faransa ke shirin kammala janye dakarunta daga Mali bayan da dakarun Barkhane suka shafe kusan shekaru 10 suna gwabza fada da mayakan jihadi a kasar.

Oumeya Ould Albakaye babban jigo a kungiyar IS a yankin Sahel, wata majiyar tsaro da ta nemi a sakaye sunanta, ta shaida wa kamfanin dillacin labaran Faransa na AFP cewa ana daukar Albakaye a matsayin wanda zai maye gurbin tsohon Shugaban IS-GS Adnan Abu Walid al-Sahrawi, wanda sojojin Faransa suka kashe a watan Agustan 2021.

Albakaye kwararre ne a kan abubuwan fashewa, shi ne shugaban yankin kungiyar a yankunan Gourma a Mali da Oudalan a makwabciyar kasar Burkina Faso. Shi ne ma ke da alhakin yawan cin zarafi da ake yi wa fararen hula a wadannan kasashe biyu da ke fama da kalubalen tsaro.