Faransa ta gamsu da rundunar G5 Sahel | Labarai | DW | 03.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Faransa ta gamsu da rundunar G5 Sahel

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron, ya goyi bayan shirin kafa rundunar yaki da 'yan tawaye a yankin Sahel da kasashen yankin ke kai a halin yanzu.

Shugaban na Faransa Emmanuel Macron wanda ya bayyana hakan a jiya Lahadi lokacin wata ziyarar da ya kai kasar Mali, ya shaida wa kasashen da ke wannan fafutukar cewa su tabbatar da aniyar ta su za ta yi tasirin da ake bukata. Kasashen da ake wa lakabi da G5 Sahel, na fama ne da karuwar barazanar 'yan bindiga da kuma suka zabura don tunkarar matsalar gaba-gadi.

Kasashen da ke cikin wannan hadakar dai sun hada ne da Chadi da Mali da Burkina Faso da Nijar da kuma kasar Mauritaniya. Shugaba Macron ya kuma ce yana sa ran rundunar, wadda zata fara da dakaru 5,000, ta kama aiki cikin watan gobe na Agusta.