Faransa: Kafa gwamnati ce mafita a Libiya
November 22, 2015Wannan shaguben na ministan tsaron Faransa Jean-Yves Le Drian ya biyo bayan wata sanarwa da Libiya ta bayar cewar, kungiyar IS na shirin tattara nata ya nata daga Syriya da niyar kafa tungarta a kasarLibiya. saboda haka ne cikin wata hira da ya yi da tashar rediyo ta Europe1 a birnin Paris, babban jami'in na Faransa ya nemi kasashe makwabta irinsu na Aljeriya da Masar da su kawo dauki don a fitar da Libiya daga halin da ta samu kanta a ciki.
Minista Le Drian ya nunar da cewar masu kaifin kishin addini da Libiya ta kunsa yanzu haka su kai mutane 4000zuwa 5000. A makon da ya gabata a karon farko Amirka ta yi musu ruwan bama-bamai, inda ta yi nasarar kashe Abou Nabil, da ake dangantawa da madagun 'yan Jihadin na Libiya.
Tun bayan hambarar da gwamnatin Moammar kadhafi a shekara ta 2011 ne Libiya ta fada cikin yaki. A yanzu haka dai gwamnatoci biyu na rikicin shugabanci a Libiya daya a Tripoli da kuma daya a Tobruk a gabashi, wacce kasashen duniya suka amince da ita.