Faransa: Bikin 14 ga watan Yuli da corona | Labarai | DW | 14.07.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Faransa: Bikin 14 ga watan Yuli da corona

A karon farko a kusan cikin shekaru 75 a Faransa an gudanar da bikin cikon shekaru 231 na yin juyin juya hali na 14 ga watan Yuli ba tare da yin faretin soji ba a dandalin Champs-Elysées saboda corona.

Kwararru a kan sha'anin kiwon lafiya sun yi kashedi kara yaduwar annobar corona a zagaye na biyu bayan kisan sama da mutane dubu 30 da cutar ta yi a cikin watannin biyu da suka gabata a Faransar. Wasu manyan likitoci sun bukaci gwamnatin da ta tilasta saka takunkumin rufe fuska ya zama dole ko'ina a cikin wuraran da jama'a ke taruwa.