Falasdinu za ta yanke hulda da Isra′ila | Labarai | DW | 22.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Falasdinu za ta yanke hulda da Isra'ila

Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas, ya ce zai yanke duk wata hulda da Isra'ila sakamakon tashin husumar da ta biyo bayan matakin Isra'ilar kan masallacin Al Aqsa mai daraja ga musulmi.

Wannan dai martani ne ganin yadda Isra'ila ta tsaya kan hana masallata shiga masallacin na birnin kudus ta hanyar tsaurara tsaro. Shugaban na Falasdinawa, ya fada a zaman majalisar ministocin kasar cewar matakin na yanke shawarar dakatar da hulda da Isra'ila ne da yawun ilahirin Falasdinawa. Ya kuma tabbatar da cewa ba zai janye ba, sai har ita ma Isra'ilar ta janye matsayinta.

Falasdinawa uku ne dai 'yan sandan Isra'ila suka halaka tare da jikkata wasu 400 a rigimar da ta kaure a jiya Juma'a. Su ma jami'an na Isra'ila sun ce Falasdinawan sun kashe mutanensu uku ta hanyar daba masu wuka a arangamar ta jiya.