1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin Isra'ila kan mayakan Hamas

Lateefa Mustapha Ja'afar
January 31, 2020

Isra'ila ta sanar da cewa ta kai wasu hare-haren ramuwar gayya, a kan mayakan Hamas na Falasdinu bayan da aka kai mata harin rokoki daga yankin Zirin Gaza.

https://p.dw.com/p/3X5zZ
Israel Nahost Sderot Gaza
Isra'ila ta yi ruwan bama-bamai kan 'yan HamasHoto: picture-alliance/dpa/I. Yefimovich

Kakakin sojojin Isra'ilan ne dai ya bayyana cewa sun yi luguden bama-bamai a kan mayakan Hamas na Falasdinu, biyo bayan wasu hare-hare da aka kai da rokoki uku daga yankin Zirin Gaza zuwa Isra'ila. Falasidinawan dai na ci gaba da nuna adawarsu da abin da shugaban Amirka Donald Trump ya kira da jadawalin zaman lafiya na karni a yankin Gabas ta Tsakiya, yayin da a hannu guda Isra'ila ta kara yawan dakarunta a kan iyakarta da yankin Zirin Gaza na Falasdinu.