Fafutukar yaki da cutar Ebola
September 18, 2014Talla
Al'ummomin kasa da kasa na ci gaba da kokarin bayar da nasu talafi kan yaki da cutar Ebola da a halin yanzu tayi sanadiyar rasuwar mutane fiye da 2400 a yankin yammacin Afirka. Tuni dai wasu daga cikin shugabannin kasashen dake fama da cutar ta Ebola suka fara nuna murnar su kan wannan mataki.