Fafutukar tabbatar da tsaro a Najeriya | Siyasa | DW | 18.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Fafutukar tabbatar da tsaro a Najeriya

A ci gaba da kokari na neman mafitar rigingimu da tada hankalin da ke neman mamaye sassa daban-daban na Najeriya, jihohin da ke da ruwa da tsaki a rikicin na neman mafita.

Kama daga Benue ya zuwa Adamawa da Jihar Taraba dai an kashe da daman gaske, cikin wata guguwa ta tada hankalin da ake dangantawa da rigingimun kabilanci a daukacin Najeriya. To sai dai kuma daga dukkan alamu idanuwa suna dada budewa ga masu mulki na kasar da ke neman hanyoyin tinkarar matsalar da kuma sannu a hankali suke fadin an kusa daidaitawa. Akwai alamun sauyin rawa a bangare na gwamnatocin da ke tunanin samun mafita rikicin abin kuma da ya mamaye wani taron majalisar tattali na arzikin kasar. Majalisar dai ta kare zamanta da  kafa wani kwamiti na gwamnoni guda tara da suka fara aiki nan take da nufin neman mafitar rikicin da ke kara tashi da lafawa ta wutar daji.

Daya kuma a cikin shawarwarin da ake saran su fito daga kwamitin na zaman sake kirkiro da burtali a sassa daban-daban cikin kasar da suka rikide ya zuwa filin noma a fadar dr Abdullahi Umar Ganduje da ke zaman gwamnan Jihar Kano wanda ya ce ya zama wajibi a tashi tsaye wajen kawo karshen tashin hankalin.

 

Sauti da bidiyo akan labarin