Faduwar Naira na shafar al′amuran rayuwa a Najeriya | Siyasa | DW | 17.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Faduwar Naira na shafar al'amuran rayuwa a Najeriya

Talakawa na ji a jika musamman ganin yadda kayan abinci suka yi tsada a kasar yayin da wasu 'yan kasuwa suka kasance ba harka saboda faduwar darajar Naira idan aka kwatanta da na kasashen waje.

Nigeria Geld Geldscheine Naira in Lagos

Naira kudin Najeriya


Bincike da Dw ta gudanar a kasuwar hada hadar ciniki na kudaden ketare ya nunar da cewa a kowace Dalar Amirka daya ana sayenta a kan Naira 360 a yayin da ake sayar da kudin gamaiyar Turai na Euro kan Naira 380 akan kowane Euro daya sai kuma Pounds na Ingila da ake sayarwa a kan kowane daya Naira 490 a kasuwar bayan fage a birnin Legos. Hakan dai na nuni da cewa har yanzu kudin Najeriya na ci gaba da faduwa warwar duk kuwa da matakin da Gwamnatin kasar ke dauka na farfado da darajar kudin .


Nigeria Symbolbild Muhammadu Buhari Anti-Korruptions-Offensive

Shugaba Buhari

To sai dai a cewar Mista Alibi Idowu wanda ke da kamfanin canjin kudade a Legos ya danganta halin da ake ciki da rashin bin doka.

"Da zarar mutane sun lura cewa gwamnati ba da gaske take ba sai komai ya tafi a kaikaice amma kuma bin doka shi ne kashin bayan cigaban kowace al'umma ga misali 'yan Najeriya da ke zuwa kasar Birtaniya sun san cewa an haramta fitsari akan tituna amma da sun dawo gida sai su cigaba da keta dokar kasa sabili da sakaci na gwamnati".

Symbolbild Afrika Markt Bunt

Yar kasuwa na dakon ciniki

Sai dai duk da haka wasu jama'ar na kallon yadda Naira ke cigaba da faduwa duk kuwa da ikirarin da gwamnati ta yi na kin rage darajar kudin kasar abin da ke shafar duk wani abu da ya shafi ta'ammali da kudi a kasar, yayin da talakawa ke ji a jika musamman ganin yadda kayan abinci suka yi tsada.

Bincike ya nuna yadda 'yan Najeriya ke faman babatu a kafafan yada labaru kan yarda fannin tattalin arzikin kasar ke shiga da kuma faduwar darajar naira a kullum rana ta Allah

Sauti da bidiyo akan labarin