1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Faduwar jarrabawar JAMB a Najeriya

July 1, 2021

Tun a ranar 25 ga watan Juni ne dai hukumar JAMB a Najeriya ta sanar da sakamakon jarrabawar, sai dai kuma batun da ke daukar hankali a yanzu shi ne yadda dalibai da dama suka yi mummunar faduwa.

https://p.dw.com/p/3vtE9

Alkalumma na nuna cewa kimanin kashi 10 kacal cikin dari na wadanda suka zauna zara jarabawar shara fagen shiga jami'a wanda galibinsu matasa ne suka sami nasara a jarabawar ta bana, yayin kashi 90 suka fadi warwas. Matasa da dama na ikirarin cewa ba rashin karatu ne ya haifar musu da rashin samun nasarar ba, inda suke ganin matsalar ta samu ne daga ita kanta hukumar ko ma wasu dalilai na daban.